Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Archbishop Gabriele Giordano Caccia wanda shi ne jakadan fadar Vaticana birnin manila na kasar Philipine, ya samu kyautar wani allo na tarihi da aka rubuta aIran, wanda yake dauke da waya daga cikin littafin Linjila aya ta 21 a cikin Luqa.
A cikin abin da ya rubuta kan wannan lamari ya bayyana cewa:
Malama Qaqvi
Hakika na farin ciki maras misiltuwa kan samun wannan allo, wanda yake da matukar muhimmanci a wurina, musamman ganin matsayin allon da kuma ranar da aka bayar da shi kyauta a gare ni, wato ranar jamhuriyar muslucni ta Iran.
Abin tuni dais hi ne, wannan allo wanda aka rubuta shi dauke da ayar Linjila, wannan aya ta yi daidai da aya ta 6 da ke cikin kur'ani a cikin surat Inshirah (Hakika lallai tsanani yana tare da sauki).