IQNA

Zaman Koyar Da Harda Da Karatun Kur’ani A Switzerland

23:38 - March 28, 2018
Lambar Labari: 3482518
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman koyar da karatu da harder kur’ani mai tsarki wanda Muhammad Mehdi Haqgoyan zai jagoranta a cibiyar Ahlul bait (AS).

 

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar Ahlul bait (AS) da ke kasar Switzerland cewa, Muhammad Mehdi Haqgoyan zai jagoranci zaman ne a ranar 31 ga watan Maris da muke ciki.

Muhimman abubuwan da zaman zai mayar da hankali kansu su ne, harder kur’ani da kuma hanyoyin karatu da salo daban-daban da ake yin amfani da shi.

Muhammad Mehdi Haqgoyan makarancin kur’ani ne dan kasar Iran wanda ya taka muhimmiyar rawa a dukkanin bangaro na tilawa, kamar yadda ya zo a matsayi na daya a duniya baki a wajen yin amfani da salo 74 na kira’a, wadanda aka sani da kuma wadanda ya kirkiro da kansa.

3702120

 

 

 

 

 

 

captcha