IQNA

Taro Mai Taken Debe Kewa Da Kur'ani A Iraki

23:43 - March 29, 2018
Lambar Labari: 3482521
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taron karatun kur'ani mai tsarki mai taken debe kewa da kur'ani a garin Basara na Iraki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da wani zaman taron karatun kur'ani mai tsarki mai taken debe kewa da kur'ani a jami'ar Imam Kazem (AS) da yankin Hayyul Ishar a cikin garin Basara.

Kasim Maliki shi ne shugaban gamayyar kungiyoyin makaranta kur'ani na jahar Basara, ya fara gabatar da jawabi a wurin, tare da bayyana manufar taro da cewa ita ce raya kwanakin watan Rajab masu albarka.

Daga cikin abubuwan da shirin ya kunsa har da sauraren karatu daga fitaccen makarancin kur'ani na duniya kuma dan kasar Iran wati Shaker Najad.

Shaker Najad shi ne ya lashe gasar kur'ani ta duniya ta sarki Abdulaziz a Makka a shekara ta 1995, inda ya zo a matsayi na daya.

3702328

 

 

 

 

 

captcha