Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, da'esh ta sanar da cewa ita ce ta tashi wata mota mai bama-bamai a wurin bincike na jami'an tsaro da ke garin Ajdabiya a gabacin kasar Libya.
Kungiyar ta Da'esh ta ce wanda ya kai harin da motar shi ne wani mutum mai suna Kudamah al-Sa'ih.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas da suka hada soja da fararen hula, yayin da wasu mutane takwas su ka jikkata.
Wannan shi ne karo na biyu da aka kai harin ta'addanci a cikin garin Ajdabiya a cikin wata guda.
Harin tara ga watan Maris ya kashe mutane uku da kuma jikkata wasu dama. Shi ma kungiyar ta Da'esh ce ta dauki alhakin kai shi.
Libya tana cikin matsalar tsaro tun a dubu biyu da sha daya da aka kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi.