Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na yanar gizo na dar-alquran.org ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da wani taron karaun ku’ani mai tsarki a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke Karbala tare da halartar makaranta kur’ani na duniya da kuma na kasar Iraki.
Sheikh Khairaddin Hadi daya ne daga cikin mambobin kwamitin kula da harkokin kur’ani na kasar Iraki, ya bayyana cewa wannan taro yana daga cikin irin tarukan da ake shiryawa a kowace shekara a idan watan rajab ya kama.
Ya kara da cewa a wannan shekara an gayyaci wasu daga cikin makaran kur’ani na kasa Iraki, kamar yadda kuma aka gayyaci wasu daga cikin makaranta na kasa da kasa, da suka hada da Sayyid Jawad Hussaini daga kasar Iran, da kuma Muhammad Mahdi Izzaddin daga kasar Lebanon.
An gudanar da karatun hubbare mai alafarma na Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala.