Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwaba News cewa, a cikin wani bayani da ta fitar, kungiyar ta'addanci ta Daesh ta yi barazanar kaddamar da hare-hare a kan mabiya addinin kirista a lokacin gudanar da bukuwansu a duniya musamman ma a kasar Masar.
An watsa wani hoto da kungiyar take yin barazana da shi, inda aka nuna wani dan ta'adda yana dauke da wuka yana shirin yanka wani farar hula.
A cikin shekarar nan Daesh ta kaddamar da farmaki a kan mabiya addinin kirista a cikin kasar Pakistan, inda suka kasha fararen hula hudu tare da jikkata wasu da dama.
Baya ga haka kuma kungiyar ta yi barazanar kaddamar da hare-hare a kan fadar Vatican ta mabiya addinin kirista, da kuma a kan paparoma jagoran mabiya addinin kirista na darikar katolika.