IQNA

23:49 - May 08, 2018
Lambar Labari: 3482642
Bangaren kasa da kasa, Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa ta samu nasarar kwato mutane sama da 1,000 daga hannun 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram wadanda ta yi garkuwa da su a jihar Borno.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar sky News ta habarta cewa Rundunar sojin ta sanar da hakan ne ta bakin daraktan hulda da jama’a na rundunar Birgediya Janar Texas Chukwu, cikin wata sanarwar da ya fitar wanda ya raba wa manema labarai inda ya ce an kwato mutanen ne a  kauyukan Malamkari, Amchaka, Walasa da kuma Gora na karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.

Rahotanni sun ce  mafiya yawansu mutanen da aka kwato din mata, kananan yara da kuma samaruka ne wadanda mayakan na Boko Haram suka hore musu kunne ko kuma tilasta musu zama 'yan kungiyar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin suke samun nasarar kwato mutanen da 'yan Boko Haram din suka yi garkuwa da su ba wadanda aka yi amanna da cewa adadinsu ya kai dubbai.

3712371

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، boko haram ، dubbai ، jihar borno ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: