Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin albayan ya bayyar da rahoton cewa, a jiya cibiyar Muhammad Bin Rashid a hadaddiyar daular larabawa mai buga kur’anai tare da cibiyar buga kur’anai ta Saudiyya za su buga tafsiran kur’ani domin rabawa ga jama’a.
Bayanin ya ci gaba da cewa bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya tare da sanya hannu kan buga kafi miliyan uku na kur’anai masu dauke da tafsiri.
Abdulrahman Bin Mu’adah Shahri shugaban cibiyar buga kur’naia a birnin Makka shi ne ya wakilci cibiyar wajen rattaba hannu kan yarjajeniyar.
Babbar manufar hakan a cewarsa ita ce samar da wata hanya da mutane za su rika gane ma’anonin ayoyin da suke karantawa.
Ya ce za a buga kur’anan ne a kowane shafi za a yi bayanin ayoyin da ke ciki daga kasa, kan dalilan saukar ayar da kuma abin da take koyarwa.
Saudiyya dai na daga cikin kasashen da suke buga tarin kur’anai suna rabawa a duniya, duk kuwa da cewa a baya-bayan nan wasu kasashen turai sun hana karbar kyautar duk wani littafi da aka buga a kasar domin kaucewa abin da suka kira yaduwar tsasauran ra’ayi da sunan addini.