IQNA

Rouhani: Iran Ba Za Taba Mika Wuya Ga Kasar Amurka Ba

23:56 - June 27, 2018
Lambar Labari: 3482789
Bangaren siyasa, shugaban kasar Iran Hassan Rauhain ya bayyana cewa, Iran ba za taba mika wuya ga bakaken manufofin Amurka ba, duk kuwa da matsin lamabra da take fuskanta.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar Iran ba za ta taba mika kai ga barazana da kuma matsin lambar shugaban Amurka, Donald Trump, ba yana mai shan alwashin cewa gwamnatinsa za ta magance matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta a halin yanzu.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a daren jiya inda ya ce duk da matsalolin da ake fuskanta, yayi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta lamunce wa al'ummar Iran din da abubuwan da suke bukata na yau da kullum.

Shugaban na Iran ya sake jaddada cewa gwamnati da kuma al'ummar Iran ba za su taba mika kai ga bakar siyasar Amurka a kokarin da take yi na cimma manufofinta ba.

Cikin 'yan kwanakin nan dai an sami tashin farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudin Iran lamarin da ya haifar da wasu 'yan zanga-zangogi da aka gudanar a Tehran a jiya ana bukatar gwamnatin da ta dau mataki musamman kan wasu 'yan kasuwa da ake ganin suna da hannu cikin hakan.

3726044

 

 

 

 

captcha