IQNA

An Halaka 'Yan Ta'addan Daesh 6 A Afghanistan

23:58 - July 05, 2018
Lambar Labari: 3482811
Bangaren kasa da , Jami'an tsaron kasar Afghanistan sun samu nasarar halaka adadi mai yawa na 'yan ta'addan Daesh da Taliban a wasu garuruwan kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da farautar 'yan ta'adda na kungiyoyin daesh da Taliban, jami'an tsaron kasar Afghanistan sun samu nasarar halaka 34 daga cikin mayakan wadannan kungiyoyi masu dauke da akidar wahabiyanci, wadanda suka addabi al'ummar kasar da hare-haren ta'addanci.

Rahoton ya ce daruruwan jami'an sojin kasar Afghanistan sun yi wa mayakan daesh kawanya ayankunan Haske mineh da kuma Achin da ke cikin gundumar Nangarhar, inda daga bisani suka afka musu musu tare da halaka wasu da kame wasu.

Kamar yadda kuma a yankunan Ab bande da Maqar, da ke cikin gundumar Gozni, dakarun na Afghanistan sun kasashe wasu 'yan ta'addan, mafi yawansu mayakan kungiyar taliban ne.

3727378

 

 

 

 

 

captcha