IQNA

23:59 - August 21, 2018
Lambar Labari: 3482912
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da sallar idi a yau a masallacin Quds tare da halartar dubban musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya habarta cewa, a yau an gudanar da sallar idi a yau a masallacin Quds tare da halartar dubban musulmi mazauna birnin.

A yayin sallar babban limamin masallacin Quds Sheikh Muhammad Hussain ya gabatar da huduba, inda ya bayyana wannan rana a masayin babbar rana ga dukkanin musulmi.

Dangane da matsayi da karamar wannan masalaci mai alfarma kuwa, malamin ya jadda cewa za su ci gaba da yin tsayin daka wajen kare martabar wannan wuri.

Dubun-dubatr musulmi ne dai suka halarci wannan salla duk kuwa da rin tsauraran matakan da Isra’ila ta dauka domin firgita masallatan.

An kammala sallar lafiya ba tare da wani yamutsi ba, kuma kowa ya koma gidansa lafiya.

3740458

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، quds
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: