IQNA

23:57 - August 22, 2018
Lambar Labari: 3482915
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da sallar idin babbar salla a yau a tsakanin hubbarorin biyu masu alfarma a Karbala.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalt daga shafin yada labarai na kafil cewa, a yau an gudanar da sallar idin babbar salla a tsakanin hubbarorin biyu masu alfarma na Imam Hussain (AS) da kuma Abbas (AS) A birnin na Karbala mai alfarma.

Bayanin ya ce mafi yawan wadanda suka halarci wannan salla dai mutanen birnin ne da kuma masu ziyara.

Sheikh Habib Alkazimi shi ne ya jagoranci sallar kuma ya huduba a wurin, inda ya yi siahara da matsayin wannan wannan rana da take a matsayin alamin sadaukantarwa.

Haka ann kuma ya bayyana matsayin koyi da abin da wannan sunna take tattare da shi, da kuma yadda ya kamata musulmi su zama masu riko da koyarwar musulunci a kowane lokaci a cikin dukkanin lamurransu na rayuwa.

3740712

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: