IQNA

23:47 - August 23, 2018
Lambar Labari: 3482919
Bangaren kasa da kasa, shugaban kungiyar ‘yan ta’addan daesh Abubakar Baghdadi ya yi wani sabon bayani da aka nada a sauti domin mabiyasa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Suzju ta kasar Turkiya ta bayar da rahoton cewa, a jiya shugaban kungiyar ‘yan ta’addan daesh Abubakar Baghdadi ya yi wani sabon bayani da aka watsa sautinsa.

A cikin bayaninsa Abubakar Baghdadi yana kiran mabiyansa da su kara zage dantse domin yin abin da ya kira jihadi, yana mai kara kwadaitar da su da abin da ya kira shahada a tafarkin Allah idan suka mutu.

Kamar yadda kuma ya jaddada musu cewa da sannu su ne za su yi nasara a jihadin da suke na daukaka a bin da ya kira Kalmar Allah.

Baghdadi wanda ya jima a boye ba a ji sautinsa ko ganin hotunsa ba, ya bayyana ne a cikin lokacin da ‘yan ta’addan daesh suke shan kashi a hannun darun Syria, inda aka murkushe su a mafi yawan yankunan da suke iko da su a da, kamar yadda a Iraki kuma an riga an murkushe su.

‘Yan ta’addan Takfiriyya masu dauke da akidar wahabiyanci suna yaki a kan al’ummar musulmi a kasashen Iraki da Syria da kuma wasu kasasen yankin.

3740784

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: