IQNA

23:50 - August 24, 2018
Lambar Labari: 3482920
Bangaren kasa da kasa, an girmama wasu daliban kur'ani mahardata su 174 a lardin Fyum na Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Abdulaziz Najjar shugaban hukumar zartarwa ta lardin fayum, ya jagoranci girmama wasu daliban kur'ani mahardata su 174 a lardin na Fyum.

Dukkanin daliban dai sun hardace kur'ani mai tsarki kuma sun kasance daga cikin masu nuna kwazo matuka a makarantunsu.

An gudanar da taron girmama daliban ne a babban dakin gudanar da taruka na lardin Fayuma  jiya, inda aka basu kyautuka da kuma allunan yabo.

3740853

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، gudunar ، Fayum
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: