IQNA

23:51 - September 11, 2018
Lambar Labari: 3482974
Bangaren kasa da kasa, wakilin gwamnatin kasar Syria majalisar dinkin duniya ya jaddada cewa za su ‘yantar da lardin Idlib.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hussamddin Ala wakilin gwamnatin kasar Syria majalisar dinkin duniya ya jaddada cewa za su ‘yantar da lardin Idlib daga mamayar ‘yan ta’ada.

Wakilin na Syria ya bayyana hakan nea zaman da kwamitin tsaro ya gudanar kan batun yunkurin da gwamnatin Syria take yin a tsarkake lardin Idlib daga ‘yan ta’addan wahabiyawa da suka mamaye lardin.

Kasashen yammacin turai suna ta hankoron ganin sun hana gwamnatin Syria korar ‘yan ta’adda daga wannan yanki, wanda shi kadai ya rage a hannun ‘yan ta’adda a halin yanzu, wadanda yanzu haka sun fara tsorata suna ta arcewa suna komawa kasashen da suka fito.

3746145

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: