IQNA

An Umarci Adel Abdumahdi Domin Kafa Gwamnati A Iraki

22:54 - October 03, 2018
Lambar Labari: 3483024
Bangaren kasa da kasa, Barham Saleh sabon shugaban kasar Iraki, ya umarci Adel Abdulahdi da ya kafa sabuwar gwamnati a kasar ta Iraki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bayan da majalisar dokokin kasar Iraki ta kada kuri'ar zaben shugaban kasa a jiya, Barham Saleh wanda dan kabilar Kurdawa ne, ya lashe zaben da gagarumin rinjaye.

Jim kadan bayan hakan kuma ya yi rantsuwar kama aiki a gaban majlaisar, yayin da shi kuma ya dora wa Adel Abdulmahdi wanda shi kuma dan shi'a ne, nauyin kafa sabuwar gwamnati, inda shi kuma zai rike mukamin firayi ministan kasar ta Iraki, wadda akasarin utann kasar mabiya mazhabar shi'a ne.

Adel Abdulmahdi dai yana da lokaci na kimanin wata guda a nan gaba domin gabatar da sunayen ministocin da ya zaba, domin gabatar da su a gaban majalisar dokokin kasar domin tantance su.

3752318

 

 

captcha