IQNA

Sabon Tsarin Hardar Kur’ani A Masar

23:15 - October 10, 2018
Lambar Labari: 3483036
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Saleh Abbas wakilin cibiyar azhar ya bayyana cewa suna da wani sabon tsari da za a bullo da shi a bangaren hardar kur’ani.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yke yin rangadi a wasu cibiyoyin kur’ania  kasar Masar, Sheikh Saleh Abbas wakilin cibiyar azhar ya bayyana cewa suna da wani sabon tsari da za a bullo da shi a bangaren hardar kur’ani da za a fara aiwatarwa nan ba da jimawa ba.

Tsarin dai zai kunshi yin amfani da kwararru kan sanayyar halayyar dan adam wajen samar da hanya da tafi dacewa da mutane masu su yin hardar kur’ani da kuma yanayinsu, domin saukaka hardar a gare su.

Shirin dai za a aiwatar da shi ne ta hanyoyin na zamani, duk kuwa da cewa za a fara ne da wasu yankuna kafin daga bisani ya isa zuwa sauran yankuna na kasar Masar.

Sheikh Saleh ya ce ko shakka babu wannan tsari zai taimaka matuka musamman ga matasa masu sha’awar hardar kur’ani.

3754819

 

 

captcha