IQNA

Khadijah Chengiz Ta Yi Rubutu Kan Kisan Khashoggi

0:00 - October 17, 2018
Lambar Labari: 3483048
Bangaren kasa da kasa Khadijah Chingiz bazawarar Khashoggi ta yi rubutu kan kisansa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Khadijah Chingiz bazawarar Khashoggi ta yi rubutu kan kisansa da ayar kur’ani mai tsarki ta 93 a cikin surat Nisa.

Ayar tana cewa duk wanda ya kashe mumini da gangan sakamakonsa shi ne wutar jahannama yana mai dawwama a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi kuma ya la’ance shi, kuma ya tanadar masa azama mai girma.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata Khadijah ta bukaci da a gudanar da bincike kan masarautar Al Saud da ke da hannu a kisansa, kamar yadda dansa ma ya bukaci da a kafa kwamiti na kasa da kasa domin gudanar da bincike kan batun.

Tashar CNN ta ce Sauduyya na shirin amincewa da kisan Khashoggi, amma za ta bayyana cewa an kashe shi ne bisa kure.

3756392

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، turkiya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :