IQNA

Taron Bayar Da Horo Kan Kur'ani A Zimbabwe

22:30 - October 24, 2018
Lambar Labari: 3483072
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan kur'ani mai tsarki a kasar Zimbabwe.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan kur'ani mai tsarki a kasar Zimbabwe a kwalejin musulunci da ke babban birnin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, karamin ofishin jakadancin kasar Iran ne ya dauki nauyin shirya wannan horo, wanda aka gayyaci dalibai musulmi domin samun horo dangane da karatu da kuma sanin hukuncin karatun kur'ani mai tsarki.

Babbar manufar wannan shiri dai itace, samar da yanayi da zai taimaka ma mabiya addinin musulunci a kasar ta Zimbabwe, wadanda kuma su ne marassa rinjaye a kasar.

Daga karshe bayan kamala bayar da horon za a bayar da kyautuka ga wadanda suka halarci zaman horon domin samun littafai da kuma abubuwan da za su taimaka musu wajen ilimin kur'ani.

3758661

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :