IQNA

22:55 - November 15, 2018
Lambar Labari: 3483128
Bangaren kasa da kasa, cibiyar muslunci ta Imam Hussain (AS) da ke birnin Admonton na kasar Canada ta dauki nauyin shirya taro mai taken tunawa da Allah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babbar cibiyar addinin muslunci ta Imam Hussain (AS) da ke birnin Admonton na kasar Canada ta dauki nauyin shirya taro mai taken tunawa da Allah a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan maulidi.

Cibiyar ta shirya wannan taro ne a matsayin daya daga cikin tarukan da take shiryawa a watan maulidi, wanda ta baiwa taken tunawa da Allah madaukakin sarki.

Babbar manufar wadannan taruka da cibiyar ke shiryawa dai ita ce, yi wa musulmi bayani kan lamurra da dama da suka shafi addinin muslunci, da kuma amsa tambayoyin mutane da ba musulmi ba da suke halartar wadannan taruka.

Wannan cibiya dai ita ce cibiyar muslucni mafi girma a wannan birni, inda musulmi masu mahanga daban-daban sukan taru a wurin domin gudanar da ayyukansu na ibda da kuma taruka, ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba.

3764192

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Canada ، imam hussain
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: