IQNA

Zaman Taron Makon Hadin Kai A Kasar Indonesia

22:55 - November 23, 2018
Lambar Labari: 3483146
A jiya ne aka gudanar da zaman taron makon hadin kai a kasar Indonesia a garin Banten a daidai lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW).

 

Shafin sadarwa na cibiyar yada al'adun musulunci ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da zaman taron ne a babban dakin taruka na jami'ar Malik Hasanuddin da ke birnin na Banten, tare da halartar malamai da kuma masana gami da daliban jami'ar.

An gabatar da jawabai ga mahalarta taron, inda malamai suka maida hankali wajen yin fadakarwa kan tarihin manzon Allah (SAW) da kuma gwagwarmayar da ya yi wajen tabbatar da addinin Allah, da kuma koyar da muuslmi darussa daga rayuwarsa mai albarka.

Jakadan kasar Iran a kasar Indonesia Mehrdad Reshshande ya gabatar da nasa jawabin a wajen wannan babban taro na maulidin manzon Allah, inda ya mayar da hankali wajen bayyana gagarumar gudunmawar da manzon Allah ya bayar wajen hada kan al'ummar musulmi, da kuma dora su kan sahihin tafarki na koyarwa ta kur'ani mai tsarki da sunnarsa, inda ya bayyana cewa hakikanin bin tafarkin sunnar manzon Allah shi ne yin koyi da shi a cikin ayyukansa.

3766354

 

captcha