IQNA

18:43 - November 27, 2018
Lambar Labari: 3483155
Bangaren kasa da kasa, an nuna tarjamar littafin addu'a na du'ul Kumail a birnin Harare na kasar Zimbabwe.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a  jiya ne aka gudanar da taron nuna tarjamar littafin addu'a na du'ul Kumail a birnin Harare na kasar Zimbabwe wanda Sheikh Abdullah Makuinja ya yi, tare da halaratr malamai da masana musulmi na kasar.

Malamin ya bayyana cewa, ya gudanar da wannan aikin ne da nufin ganin ya yi wani aiki domin son ahlul bait (AS) wanda kuma wannan addu'a tana nuna hakikanin yadda ahlul bait (AS) wajen kaskantar da kai ga Allah da ganin girmansa da kuma bauta masa.

An tarjama littafin ne zuwa harshen Shouna wanda ake amfani da shia  kasar da ma wasu kasashe makwafta, domin amfanin wadanda suke fahimtar harshen.

Wannan littafi za a raba shi a masallatai da makarantun addini gami da cibiyoyin addinin muslunci a birnin an Harare da kuam wasu garuruwa na kasar ta Zimbabwe.

Daga karshe Jakadan Iran a kasar Zimbabwe Reza Askari ya gabatar da nasa jawabin, tare da jaddada cewa za su dauki nauyin buga kwafi mai yawa na wannan tarjama, domin amfanin musulmin kasar ta Zimbabwe nan ba da jimawa ba.

3767148 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، amfanin ، jaddada ، Zimbabwe
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: