IQNA

Za A Bude Makarantun Kur’ani Guda 24 A Masar

23:56 - December 19, 2018
Lambar Labari: 3483232
Bangaren kasa da kasa, ma’ikatar kula da harkokin addini a Masar ta ce za a bude wasu makarantun kur’ani mai tsarki guda 24 kafin karshen shekarar da muke ciki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin wani bayani da ta fitar, ma’ikatar kula da harkokin addini a Masar ta ce za a bude wasu makarantun kur’ani mai tsarki guda 24 kafin karshen 2018 da muke ciki.

Bayanin ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ya ce, idan aka kammala aikin gina wadannan makarantu daga nan zuwa karshen shekara, adadin makarantun kur'ani da suke karkashin kulawar wannan ma'aikata za su kai 788.

Haka nan kuma bayanin yakara da cewa, idan aka kammala aikin gina makarantun, za a sanar da iyayen yara domin su kawo yaransu a yi rijistar sunayensu kafin lokacin fara karatu.

3774096

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha