IQNA

Netanyahu Na Ci Gaba Da Batun Makaman Hizbullah

23:58 - December 19, 2018
Lambar Labari: 3483233
Netanyahu firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi da’awar cewa Hizbullah ta dakatar da kera makamai saboda ya tona asirin hakan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa, Benjamin Netanyahu firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi da’awar cewa Hizbullah ta dakatar da kera makamai masu sarrafa kansu a cikin kasar Lebanon, sakamakon abin da ya kira tona asirin hakan da ya yi a cikin watan Satumban da ya gabata.

Ya ce Tun bayan da ya yi magana kan wannan batu Hizbullah ta dakatar da kera wadannan makamai a cikin kasar Lebanon, saboda haka yanzu irin wadannan makaman kadan ne a hannun Hizbulla.

Ya kara da cewa suna da niyyar ci gaba da kera su a wasu wuraren, amma gwamnatin Isra'ila ba za ta bari ba, za ta yi dukkanin abin da za ta iya yi domin hana Hizbullah ci gaba da kera makamai masu hadari ga makomar Isra'ila.

3773999

 

 

 

 

captcha