Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da taron kammala wani shiri nan a kusanto da fahimta tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba a Masar, inda aka girmama wadanda suka gudanar da shiri mai taken “Muhammad Annabin ‘yan adamtaka” a bayan kasa.
An girmama mambobi 55 ne kawai daga cikin wadanda suka gudanar da wannan kamfe, daga cikin wadanda aka girmama akwai manyan malamai da limamai da kuma masana.
Sheikh Muhammad Al-ash daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini a yankin Sinai ya bayyana a wajen taron cewa, akwai limamai kimanin 800 da suka shiga cikin wanann kamfe, kuma sun yi nasu kokarina dukknin masallatai da cibiyoyin addini da suke jagoranta.
Y ace babbar manufar wannan kamfe dai ita ce, yaki da tsatsauran ra’ayin addini a cikin muuslmi, tare da bayyana wa al’ummomin duniya hakikanin yadda musulunci da manzon Allah ya zo yake, wanda kuma manzon Allah shi ne ya koyar da dukkanin kyawan halaye da dan adam ke bukata a rayuwarsa, kamar yadda kuma ya koyar da musulmin zaman lafiya da kowa, domin ko da yakokin da manzon Allah ya yi dukkansu sun zo ne a matsayin kare kai daga masu cutar da musulmi.