Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan mataki da wadannan ‘yan majalisar dokokin Amurka biyu suka dauka ya bakanta ran Isra’ila matuka.
Baya ga haka kuma wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Amurka sun nuna damuwa matuka dangane da yadda wadannan ‘yan majalisar suka nuna matsayinsu na kiyayya da Isra’ila a fili.
A lokacin da suke bayani sun bayyana cewa, dukkanin matsalolin da ake fuskanta tsakanin yahudawa da Palastinawa gwamnatin Isra’ila ce ta hadda su.
Kungiyar haramta kayan Isra’ila BDS dai wasu Falastinawa da kuma masu fafutuka a duniya suka kafa ta, kuma kungiyar tana yin kira ne da a kaurace wa dukkanin kayan da Isra’aila take samarwa, domin kuwa ita gwamnati ce ta wariya kamar irin gwamnatin wariya da aka yia kasar Afrika ta kudu.