IQNA

22:49 - February 12, 2019
1
Lambar Labari: 3483366
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasrullah.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a jiya ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasrullah a birnin Beirut.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a yayin ganawar, ministan harkokin wajen Iran ya bayyana farin cikinsa dangane da kafa gwamnati a kasar Lebanon, tare da yin fatar samun nasar gudanar da ayyukanta.

Haka nan kuma ya bayyanacewa, kasarsa a shirye take ta ci gaba da taimaka ma kasar Lebanon a dukkanin bangarorin da take bukatar taimako.

Shi ma a nasa bangaren Syyid Hassan nasrullah yay aba da ziyarar ta Zarif, tare da bayyana goyon baya da kuma taimakon da Iran take baiwa kasar Lebanon da cewa, shi ne baban sirrin samun dukkanin nasarori a kan makiyan kasar musamman yahudawan sahyuniya.

Daga karshe Sayyid Nasrullah ya yi fatan samun nasara a cikin dukkanin lamurra da Iran ta sanya  agaba, da kuma taya dukkanin al’ummar kasar murnar zagayowar lokacin bukukuwan cikar shekaru arba’in na samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar.

3789352

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
ABUBAKAR YUSIF
0
0
Allah ya saka da wannan ziyarar ilahi ajeb
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: