IQNA

23:00 - February 17, 2019
Lambar Labari: 3483381
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya karyata batun cewa kungiyar tana da mayaka a cikin Venezuela.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, babban magatakardar kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi na ranar tunawa da jagororin gwagwarmaya da su ka yi shahada

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa; Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun yi dukkanin abin da za su iya, amma kawancen gwgawarmaya ne zai iya ayyana makomar wannan yankin domin tuni ya shiga cikin fagen samun nasara

Sayyid Hassan Nasarallah ya kara da cewa; Karfin da kawancen gwagwarmaya yake da shi, bai takaita a cikin makami ba kadai, yana tattare da akida da kuma azama, kuma matukar gwgawarmayar tana da wadannan abubuwan, babu yadda za a yi makiya su iya fuskantarta

Da yake magana akan zagayowar cikar shekaru 40 daga cin nasarar juyin musulunci na Iran, shugaban kungiyar ta gwgawarmaya ya ce; Miliyoyin al'ummar Iran sun mayar da martani akan dukkanin takunkumai da yakin tattalin arziki da aka kakabawa Iran, ta hanyar fitowar da su ka yi domin raya ranar cin nasarar juyi

Dangane da taron Warsaw na kasar Poland akan gabas ta tskaiyar kuwa, Sayyid Nasrallah ya ce; Manufarsa ita ce fito da boyayyar alakar Natanyaho da kasashen larabawa ne a fili.

Akan yakin kasar Yemen, kuwa jagoran na kungiyar Hizbullah ya ce; Yaki ne na Haramtacciyar kasar Isra'ila da Amurka, wanda kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa suke aiwatarwa.

3790638

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: