IQNA

22:35 - February 26, 2019
Lambar Labari: 3483406
Shugaban kasar Iran din ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar bakuncin takwaransa na kasar Syria, Basshar Assad wanda ya kawo ziyara Iran.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaban na kasar Iran ya bayyana nasarar da gwamnati da al’ummar Syria su ka samu akan ‘yan ta’adda da cewa tana da kima da muhimmanci.

Shugaba Hassan Rauhani ya kuma kara da cewa; Iran a shirye take ta taimaka wajen sake gina kasar Syria da yaki ya lalata.

A nashi gefen shugaban kasar ta Syrai ya ce;gwamnati da al’ummar Syrai suna yi wa jagoran juyin juya halin musulunci na Iran godiya, haka nan gwamnati da kuma al’ummar Iran saboda taimakon da su ka baiwa Syria a fada da ta’addanci.

Shugaban na kasar Syria ya kuma abin da ya kawo shi Iran shi ne ya yi godiya.

3793361

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: