IQNA

23:37 - April 03, 2019
Lambar Labari: 3483513
Bangaren kasa da kasa, a yau ne ake gudanar da taron ranar Mabas a masallacin Khatamul Anbiya a Moscow.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau ne ake gudanar da taron ranar Mabas  ranar tunawa da aiko manzon Allah a masallacin Khatamul Anbiya a Moscow na kasar Rasha.

Za a fara taron ne bayan sallar Magriba da Isha’I, inda za a yi adduoi da kuma jawabai, Hojjatol Islam Akbari Sadiri ne wakilin jagoran juyin juya halin musluncia  kasar Rasha, wanda kuma shi ne zai gabatar da jawabi.

Yau ranar 27 ga watan Rajab ita ce ranar aiko manzon Allah (SAW) da sakon addinin muslunci zuwa ga talikai na duniya baki daya, domin shiryar da su zuwa haske na tsira.

3800778

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، haske ، tsira
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: