IQNA

22:26 - April 04, 2019
Lambar Labari: 3483516
Bangaren kasa da kasa, Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana takunumar Amurka akan kasar Iran da cewa suna matsayin aikin ta’addanci ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa; Takunkuman da kasar Amurka take kakabawa Iran suna a matsayin ta’addanci ne na tattalin arziki.

Ministan harkokin wajen na Iranwanda ya wallafa wannan sakon a shafinsa na Twitter, ya kuma ci gaba da cewa:Siyasar matsin lamba da gwamnatin Trump take yi akan Iran tana cin karo da kudurin Majalisar Dinkin Duniya, kuma tana kawo cikas a ayyukan da kungiyar agaji ta “Red Crecent’ take yi na taimaka wa mutanen da ambaliyar ruwan sama ta rutsa da su.

Muhammad Jawad Zarif ya ci gaba da cewa; Takunkuman na Amurka sun kunshi haramtawa kungiyar agajin samun jiragen sama masu saukar angulu da ake amfani da su wajen ayyukan ceto.

Zarif ya bayyana takunkuman na Amurka da cewa, baya ga kasantuwar su a matsayin yakin tattalin arziki, suna kuma daidai da ta’addanci na tattalin arziki.

 

3800944

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: