IQNA

22:24 - April 07, 2019
Lambar Labari: 3483529
Babban hafsan sojojin kasar Libiya janar Khalifa Haftar ya sanar da fara kai hare-hare kan Sojojin gwamnatin hadin kan ‘yan kasar ta sama a  Tripoli babban birnin kasar

Kamfanin dillancin labaran iqna, Duk da kiraye-kirayen da Duniya ke yiwa janar Khalifa Haftar na dakatar da ayyukan soja kan Tripoli babban birnin kasar, da alama ya yi kunan uwar shegu.

Kasashen Duniya da dama da kwamitin sulhu na MDD duk sun yi kira ga janar Khalifa Haftar ya dakatar da shirinsa na kwace birnin Tripoli, amma dai da alama ya yi watsi na wannan bukata, domin a wannan Lahadi babban hafsan sojojin kasar ta Libiya ya bawa sojojin nasa umarni da su yi amfanin da tsohon filin sauka da tashin na birnin Tripoli da suka kwashe daga sojojin gwamnatin hadin kan kasar, wajen kai hare-haren kan sansanoninsu.

Tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne sosojin da ke biyayya ga Khalifa Haftar da ke rike da gabascin kasar ta Libiya suka yunkuro a anniyarsu ta karbar babban birnin kasar ga gwamnatin hadin kan kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Kafin hakan dai Sojojin sun bukaci sojojin dake biyayya da gwamnatin hadin kan kasar da su yi saranda su kuma daga farin gyale dake nuna alamar meka wuya ga dakarun na Janar Haftar, da a cewar su hakan shi zai kaucewa zubar da jini a kasar.

Da alama kuma wannan kira ya samu karbuwa daga wani bangare na dakarun dake biyayya da gwamnatin hadin kan kasar, inda rahotani suka bayyana wani tsage da Sojojin sun marawa Janar Khalifa Haftar baya.

3801377

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، janar ، Khalifa Haftar ، Libya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: