IQNA

23:55 - April 11, 2019
Lambar Labari: 3483541
Bayan shekaru talatin a karagar mulkin kasar Sudan, sojojin kasar sun sanar da hambarar da gwamnatin shugaban kasar, Omar al-Bashir da kuma tsare shi, bugu da kari kan sanar da gwamnatin rikon kwarya ta shekaru biyu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ministan tsaron kasar Laftanar Janar Awad  ne ya sanar da hakan a wani jawabi da yayi inda ya sanar da kawo karshen gwamnatin al-Bashir din ta tsawon shekaru talatin da kuma tsare shi a wani waje da bai bayyana ko ina ba ne.

Har ila yau kuma sanarwar sojin ta sanar da kafa dokar ta baci na tsawon watanni uku a kasar, kamar yadda kuma sojojin za su ci gaba da kula da kasar da kuma shirye-shiryen mika mulki cikin shekaru biyu, haka nan kuma sun sanar da dakatar da kundin tsarin mulkin kasar.

Kifar da gwamnatin Bashir din ta zo ne sakamakon zanga-zangar da al’ummar kasar suka dinga yi tsawon watanni da bukatar ya sauka daga karagar mulki.

To sai dai kungiyoyin da suka jagoranci zanga-zangar musamman kungiyar Sudanese Professionals Association sun yi watsi da sanarwar soji da cewa babu wani abin da ya sauya, don haka suka kirayi masu zanga-zangar da su ci gaba da zanga-zangogin na su har sai an biya musu bukatunsu.

3802892

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، musamman ، soji
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: