IQNA

23:54 - April 19, 2019
Lambar Labari: 3483559
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da babban taron Nisf Sha’aban a cibiyar Imam Hussain (AS) da ke birnin Edmonton na kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ana shirin gudanar da babban taron Nisf Sha’aban a cibiyar Imam Hussain (AS) da ke birnin Edmonton na kasar Canada, tare da halartar masoya ahlul bait (AS).

Taron zai fara ne daga gobe Asabar, inda za a gabatar da jawabai kan muhimmancin wannan rana mai albarka, wadda a cikinta aka haifi sahibul asr amincin Allah ya tabbata a gare shi.

A daren yau ana gudanar da wasu tarukan a wannan bababr cibiya ta addini da birnin na Edmonton, da suka hada da addu’oi da kuma tafsirin surar yasin.

3804794

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Canada ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: