IQNA

22:54 - April 26, 2019
Lambar Labari: 3483580
A safiyar yau yahudawan daruruwan yahudawan sahyuniya suka kutsa  kai a cikin harabar masallacin Aqsa mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, da kimanin 7 na safiyar yau agogon Quds, yahudawan sahyuniya masu tsatsauran kimanin su 320 suka afka a cikin harabar masallacin mai alfarma.

Wannan dai na zuwa ne kamar yadda yahudawan suka saba yi domin tsokanar Falastinawa mausulmi mazauna birnin Quds, inda kafin lokacin daruruwan ‘yan sandan Isra’ila suka kafa shingayen tsaro, domin hana Falastinawa isa wurin, domin kada su nemi bayar da kariya ga masallacin mai alfarma.

Daruruwan yahudawan sun kutsa kai a cikin harabar masallacin mai alfarma ne a yau, tare da dandazon jami’an tsaron Isra’ila dauke da muggan makamai da suke ba su kariya.

Keta alfarmar wurare masu tsarki na muuslmi a birnin da sauran yankuna na Palastinu ya zama jiki ga yahudawan sahyuniya, a daidai lokacin da wasu daga cikin sarakunan larabawa ke ta hankoron kulla alakar diflomasiyya da Isra’ila.

3806435

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: