IQNA

23:55 - May 12, 2019
Lambar Labari: 3483633
Bangaren kasa da kasa, wasu abubuan sun fashea wata tashar jiragen ruwa a hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar ad arahoton cewa, wasu abubuwa sun fashe a tashar jiragen ruwa ta Al-Fujairah na Hadaddiyar daulolin larabawa ko UAE a safiyar yau Lahadi, wacce daga baya ta yi sanadiyyar tashin gobara da ta cinye jiragen rowan daukar man fetur guda 7 a tashar.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon c eta bayyana wannan labarin, ta kuma kara da cewa har ya zuwa lokacin bada labarin ana kokarin kashe gobarar da ta taso bayan facewar.

Rahotannin basu bayyana musabbin facewar ba, da yiyuwar samun hannun yan ta’adda a cikinsa ba.

Amma hukumomin tashar jiragen ruwa ta Al-Furaija da kuma daraktan mai kula da harkokin tsaro na cikin gida a Fujarai Brigadier Ali Ubaid al-Taniji duk sun musanta cewa akwai wata facewa a tashar jiragen ruwa.

3810992

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: