IQNA

23:59 - May 13, 2019
Lambar Labari: 3483637
Bangaren kasa da kasa, an bude cibiyar koyar da kur'ani a birnin Birmingham da ke ksar Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Birmingham mail ya bayar da rahoton cewa, a jiya an bude cibiyar koyar da kur'ani a birnin Birmingham, domin gudanar da ayyuka da suka shafi kur'ani.

Wannan cibiya za ta kunshi bangarori daban-daban da za su kasance wuraren bayar da karatu da suka hada da ajujuwa guda shida, da kuma wurin taro gami da masallaci.

Tun a shekara ta 1993 aka kafa cibiyar (QAF) da ke kula da lamurran kur'ani mai tsarkia  kasar ta Birtaniya.

Masu kula da sabuwar cibiyar sun ce baya ga ilmomin kur'ani mai tsarki, za a rika koyar da wasu ilmomi na addini da kuma adabin larabci a wurin.

3811135

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، birmingham ، Birtaniya ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: