IQNA

23:55 - May 15, 2019
Lambar Labari: 3483643
Bangaren kasa da kasa, wakilan ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Oman suna halartar bababn baje kolin kur'ani mai tsarki karo na ashirin da bakawai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Khalid Tarudi babban daraktan cibiyar bincike ta addini a birnin Qirawan na Tunisia ya bayyana a wajen taron baje kolin kur'ani na duniya cewa, gudanar da irin wannan babban taro dama ce babba ga mahalrta domin samun musayar ra'ayoy kan lamurra da dama da suka shafi musulmi.

Muhammad Shafi Zal daga kasar Malayzia da yake halartar taron ya bayyana cewa kasarsa tana bayar da muhimmanci ga lamrra da suka shafi yada koyarwar kur'ani a kasa.

Faiz Bin Marhun Alhadi daga kasar Oman ya bayyana cewa, ana samun gagarumin ci gaba  akasarsa ta fuskacin harkokin kur'ani, inda a halin yanz awai cibiyoyi da dama da suke gudanar da harkoki a wannan bangare.

A wajen wannan baje kolin kur'ani na kasa da kasa dai baya ga nuna kwafi-kwafi na kur'ani a wurin,a kwai kuma littafai da suka hada da tafsirai da kuma sauran littafai da aka rubuta kan ilmomin kur'ani.

 

 

3811332

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: