IQNA

23:57 - May 21, 2019
Lambar Labari: 3483662
Bangaren kasa da kasa, an bude bababr gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya mai take gasar sarki Muhammad na shida a birnin Ribat na Morocco.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na ar.yabiladi.com ya bayar da rahoton cewa, an fara gudarnar da bababr gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya ta kasar Morocco.

Sayyid Mahdi Bilhadr shugaban kwamitin shirya gasa na kasa ya bayyana cewa,  wanann gasa ana shirya ta duk shekara, kuma a wannan shekara kamar sauran lokuta baya za ta kunshi bangarorin da aka saba.

Daga ciki akwai bangarorin tilawa da kuma harda ta hizb 5 bisa tsarin karatu na kasar Moroco, sai kuma hizb 5 bisa tsarin karatu da ake amfani da shia  duniya.

Bayan kammala gasar zuwa jibi za a bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka nuna kwazoa  wannan gasa ta sari Muhammad na shida.

 

 

3813430

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: