IQNA

21:20 - May 22, 2019
Lambar Labari: 3483666
Ma'aikatar cikin gidan kasar Masar ta sanar da rusa tashoshin 'yan ta'adda a garin Al'arish tare da hallaka 16 daga cikinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna,  ya nakalto ma'aikatar cikin gidan kasar Masar na cewa jami'an tsaron kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 16 a yayin wani farmaki da suka kai maboyar 'yan ta'addar dake garin Al-arish na yankin tsibirin Sinai dake arewacin kasar.

Sanarwar ta ce jami'an tsaron sun samu bayyanan sirri ne kan wani yunkurin 'yan ta'addar na kai hari kan wasu manyan cibiyoyi da kamfanonin kasar, don haka, kafin aikata wannan aika-aika, Sojojin suka kai musu farmaki tare da samun nasarar rusa ciboyiyon nasu.

Tun a shekarar dubu biyu das ha uku kasar Masar ta fada cikin matsalar tsaro bayan da Sisi ya yi wa zababben shugaban kasar juyin milki, lamarin da ya fuskanci rashin amincewa na 'yan kasar musaman ma mabiya kungiyar 'yan uwa musulmi wacce ita ce ta kai Mursin kan karagar milki.

 

3813635

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، musamman ، karaga ، Masar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: