Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kotun ta sanar da yanke wannan hukunci ne bayan tabbatar da cewa dukkanin mutanen 3 mambibi na kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS, wadanda suke da hannu wajen kisan dubban mutane a kasar ta Iraki.
Kotun ta sanar da cewa mutanen suna da damar daukaka kara a cikin kwanaki 30 daga lokacin yanke hukuncin.
An dai kame mutane ne a cikin kasar Syria bayan da suka sadada cikin kasar daga Iraki, daga bisani aka mika su ga kasar Iraki.
Wannan shi ne karon farko da aza zartar da hukuncin kisa kan wasu ‘yan ta’adda yan kasar Faransa a cikin kasar Iraki