IQNA

A Najeriya Mutane Dubu 20 Sun Bar Gidajensu

23:56 - May 29, 2019
Lambar Labari: 3483683
Majalisar dinkin duniya ta fitar da rahoton cewa a wasu yankuna na arewa maso yammacin Najeriya, mutane kimanin dubu 20 sun bar muhallansu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta gabatar, an bayyana cewa sakamakon matsalolin tsaro a wasu yankuna arewa maso yammacin Najeriya, dubban mutane da ke a kauyuka da suke kusa da iyaka da jamhuriyar, sun shiga cikin jamhuriyar Nijar domin tsira da rayukansu.

Rahoton ya ce, wadannan matsalolin tsaro kuwa sun hada da sace jama’a domin karbar kudaden fansa, da kuma hare-hare da ake kaiwa kan mutane a kauyuka tare da yi musu kisan gilla, wanda hakan yafi kamari nea jihar Zamfara, yayin da kuma a halin yanzu lamarin ya isa har zuwa wasu yankuna a cikin jihohin Katsina da kuma Sokoto.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majaliasr dinkin duniya ta ce tuni jami’an suka isa wuraren da aka tsugunnar da mutanen a cikin jamhuriyar Nijar, tare da aikewa da kayyakin da ake bukata cikin gaggawa.

3815386

 

 

captcha