IQNA

14:40 - May 30, 2019
Lambar Labari: 3483685
Msulmi da larabawa mazauna kasar Sweeden na shirin gudanar da tarukan ranar Quds a gobe Juma’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin wani bayani na hadin gwiwa da kungiyoyin musulmi da na laraba da kuma Falastinawa mazauna kasar Seeden suka fitar, sun sanar da cewa a gobe za su gudanar da tarukan ranar Quds a birane daban-daban na kasar.

Bayanin ya ce, tarukan za a gudanar da su ne a cibiyoyi daban-daban na musulmi, da kuam dakunan taruka a wasu biranan, inda za a gabatar da jawabai dangane da ranar Quds ta duniya.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, tarukan na wanann shekara za su banbanta da sauran tarukan da aka saba gudanarwa a kowace shekara, inda a wanann karon mafi yawan jawaban da za a gabatar a wuraren tarukan, za su fi mayar da hankali ne a kan batun yarjejeniyar karni.

Al’ummomin muuslmi da na larabawa da dama a duniya, suna kallon abin da ake kira da yarjejeniyar karni a matsayin wani sabon salon yaudara, da ke neman mayar da Falastinawa karkashin danniyar Isra’ila, tare da ci gaba da mamaye musu kasa a hukumance.

 

3815646

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ranar quds ، sweeden
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: