IQNA

Masu Gangami Fiye Da 60 Aka Kashe A Sudan

23:53 - June 05, 2019
Lambar Labari: 3483713
Rahotanni daga kasar Sudan na cewa adadin mutanen da aka kashe daga cikin masu gudanar da gangami a cikin kwanki uku ya kai 60.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran Anatoli Anatoli ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama a Sudan sun bayar da bayanai da ke cewa, adadin mutanen da aka kashe ya zuwa cikin kasa da kwanaki hudu ya kai mutum 60.

Bayanin ya ce wannan lamari sakamako ne na irin matakan da majalisar sojojin kasar ta dauka na murkushe masu neman ‘yanci da kuma samun makoma ta demukradiyya maimakon mulkin kama karya.

Da farko dai sojin sun samar da dakatar da duk wata tattaunawa tare da bangarorin siyasar kasar, dangane da kafa gwamnatin rikon wadda za ta shirya zabuka a kasar a nan gaba.

Sakamakon matsin lamba da yin tir da Allawadai da matakin da sojojin kasar ta Sudan suka dauka na yin kisa a kan fararen hula masu gangamin na lumana, hakan yasa a jiya shugaban majalisar sojojin ya dawo ya sake yin kira zuwa tattauwa tsakaninsu da jam’iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula.

 

3817330

 

http://iqna.ir/fa/news/3817330

captcha