IQNA

22:04 - June 08, 2019
Lambar Labari: 3483720
Rahotanni daga Sudan na cewa an cafke wasu jiga jigan masu zanga zanga guda biyu, sa’o’I kadan bayan ganawarsu da firaministan Habasha Abiy Ahmed wanda ya kai ziyara kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya habarta cewa, bayanai daga Sudan  na cewa an cafke wasu jiga jigan masu zanga zanga guda biyu, sa’o’I kadan bayan ganawarsu da firaministan Habasha Abiy Ahmed wanda ya kai ziyara Khartoum da nufin sasanta rikicin da ake fama dashi a kasar, tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar ta Sudan.

Bayanai da masu aiko da rahotanni suka samu daga makusantan mutanen biyu sun ce an cafke Mohamed Esmat jagoran kawancen masu fafatukar samar da sauyi  Mohamed Esmat, da kuma Ismaïl Jalab sakatare janar na kungiyar ‘yanto Sudan, bayan ganawarsu da firaminsitan na Habasha da yammcin jiya Juma’a.

Wani mamba a kungiyar ta ALC, ya shaidawa manema labarai cewa wasu matane dauke da makamai ne suka cafke jagoran nasu bayan sun fito daga ofishin jakadancin Habasha, ba tare da kuma da yi musu karin bayani ba.

Shi kuwa Ismaïl Jalab, an cafke shi ne a cikin daren jiya wajen karfe uku na dare, kamar yadda wani mamba a kungiyar ta SPLM ya sanar, sannan kuma a cewarsa sunyi awan gaba da kakakin kungiyar.

Shi dai firaminsitan na Habasha Abiy Ahmed, ya yi kiran da a gaggauta komawa kan tsarin demokuradiyya, bayan ganawa da sojojin dake rike da mulki da kuma wakilan masu bore a kasar ta Sudan.

3817738

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sudan ، habasha ، Abiy Ahmad
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: