IQNA

23:51 - June 13, 2019
Lambar Labari: 3483732
Firayi ministan kasar Japan Shinzo Abe ya gana da jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei a safiyar yau Jagoran juyin juya halin masa cewa babu yiwuwar tattaunawa da Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau firayi ministan kasar Japan Shinzo Abe, ya ziyarci jagoran juyin juya hain musulunci Ayatollah sayyid Ali khamenei.

Bangarorin biyu dai sun tattauna kan muhimamn batutuwa da suka hada da bunkasa alaka tsakanin Iran da Japan a bangarori daban-daban, kamar yadda kuma suka tattauna a kan wasu batutuwa na siyasar yankin da ma na kasa da kasa.

Baya ga haka kuma sun tatatuna kan hnkoron da Amurka take na neman ganin ta shiga tattaunawa tare da Iran, bayan da ta fice daga yarjejeniyar nukiliya, tare da kakaba takunkumai kan kasar ta Iran.

Jagoran y ace Iran ba za ta sake maimaita irin wannan tattanawa da Amurka ba, domin kuwa bata da wani amfani ga kasar.

Ya ce ko da takunkumin Amurka Iran za ta samu ci gaba a dukkanin bangarori, domin kuwa dukaknin ci gaban da ta samu cikin shekaru arbain cikin takunumin Amurka ta same shi.

Ya ce abbau wata kasa ta duniya da za ta yarda da irin wannan tattaunawa da Amurka take bukatar yi da Iran.

Tun ajiya ne dai firayi ministan kasar ta Japan ya fara ziyarar aiki ta yini biyu a kasar Iran, indaajiya ya gana da shugaban Iran kuma suka cimma matsaya kan batutuwa daban-daban, da suka hada shirin Japan na saka hannayen jari a ayyukan babbar cibiyar iskar gas ta Iran da ke kudancin kasar.

 

3819076

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: