IQNA

23:59 - July 05, 2019
Lambar Labari: 3483808
Palasdinawa hamsin ne sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila su ka jikkata a yayin Zanga-zangar nuna kin jinin mamaya akan iyakar yankin Gaza.

Kamfanin dillanicn labaran iqna, Ministan kiwon lafiya a yankin Gaza, ya bayyana cewa; Sojojin hamratacciyar kasar Isra’ila sun bude wuta akan masu Zanga-zanga a Gaza, tare da jikkata wasu mutane 19.

Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kara da cewa; Sauran palasdinawa 31su ka sami raununa mabanbanta.

Mai Magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiya ta Palasdinawa ya bayyana cewa; daga cikin wadanda ‘yan sahayoniyar su ka jikkata da akwai ma’aikatan kiwon lafiya 8 da kuma wani dan jarida.

A kowace juma’a Palasdinawa suna gudanar da Zanga-zanga akan iyaka da yankin Palasdinawa dake karkashin mamaya da kuma Gaza, domin tabbatar da hakkinsu na komawa kasarsu tag ado. Tun daga ranar talatin ga watan Maris na shekarar da ta gabata ne dai palasdinawa su ka mayar da Zanga-zangar ta shekara-shekara zuwa kowane mako.

 

 

3824544

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، plestine
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: