IQNA

23:52 - July 17, 2019
Lambar Labari: 3483850
Babban lauya a Najeriya mai kare Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi kira ga gwamnati kan ta saki malamin domin aiwatar da umarnin kotu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin  thenationonlineng cewa, Femi Falana abban lauya a Najeriya mai kare Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi kira ga gwamnati kan ta saki malamin domin aiwatar da umarnin kotu kamar yadda ta bayar da umarni a baya.

a daya bangaren kuma rahotani daga birnin Abuja sun bayyana cewa magoya bayan harkar muslunci na ci gaba da zanga-zangar lumana na meman a saki jagoransu shekh Ibrahim El Zakzaky.

Rahoton ya ce an fara jerin gwanon ne daga unguwar Nitel Junction, inda magoya bayan harkar muslucni da dama da ke cikin jerin gwanon suke rera taken neman a saki shekh Ibrahim Yakubu El zakzaky.

Ko a jiya talata ma jami'an tsaron jihar kaduna sun farwa magoya bayan harkar muslunci a yayin da suke zanga-zangar lumana na neman a saki shekh Elzakzaky, tare da kashe mutum guda da kuma jikkata wasu da dama na daban.

3828018

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Falana ، lauya ، Najeriya ، Zakzaky
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: