IQNA

23:49 - July 21, 2019
Lambar Labari: 3483866
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Masar ta sanar da 'yan kasar cewa kada su yi amfani da visar da ake samu ta yanar gizo domin zuwa aikin hajji.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, mahukuntan kasar Masar sun sanar da cewa, visa ta kasar Saudiyya da ake bayar ta hanyar yanar gizo ba za ta yi amfani a wurin aikin hajji ba.

A kan haka mahukuntan na Masar suka kirayi dukkanin 'yan kasar wadanda suke da niyyar sauke faralia  shekarar bana, da su yi amfani da visa da suka samu ta hanyar da ake bayarwa kai tsaye hannu da hannu.

Wannan an zuwa ne bayan da mahukuntan kasar ta Saudiyya da suka bayar da visa ga dubban daruruwan maniyyata ta hanayar yanar gizo, suka dawo suka sanar da cewa ba za a yi aiki da ita ba.

Yanzu haka dai ma'aikatar kula da shige ta saudiyya ta sanar da cewa, dukkanin alhazan da suka isa kasar domin aikin hajji da suka samu visar kasar ta hanyar yanar gizo za a dawo da su.

3828470

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، visa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: