IQNA

Rouhani: Iran Bata Taba Yin Watsi Da Batun Tattaunawa Ba

23:39 - July 24, 2019
Lambar Labari: 3483873
Bangaren siyasa, Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya bayyana cewa gwamnatinsa bata taba yin watsa ba wajen yin amfani da duk wata irin dama ta tattaunawa ba, kuma ba taza yin fashi ba ga hakan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cewar Shugaba Rohani, muddin yana jan ragamar gwamnatin zartaswa ta Iran, suna a shirye koda yaushe don tattaunawa amma ta gaskia, da adalci, domin shawo kan duk wasu matsaloli.

Saidai kuma a cewarsa, hakan ba yana nufin mu durkusa ba da sunan tattaunawa, a wasu irin tattaunawa ba.

A daya bangare kuma da ya tabo, batun yadda Iran ta fara dakatar da aiki da wasu sharuddan da yarjejeniyar nukiliya Iran ta cimma, shugaban Rohani y ace yanzu haka suna kan tattaunawa da kasashen turai da wasu kasashen duniya, saidai har yanzu ba’a cimma gurin da ake so ba.

A yanzu dai Iran nan na shirin daukan mataki na ukku, da ya shafi matakin data dauka na dakatar da aiki da wasu daga cikin sharudda da yarjejeniyar ta 2015 ta tanada.

Kan halin da ake ciki a tekun golfe, da tekun Oman da kuma mashigar ruwan Hormoz, shugaban Ruhani ya nanata cewa,mashigar na da matukar mahimmanci, sannan tabbatar da tsaron ya rataya ga Iran da kasashen dake kewaye, don ahak ba zasu lamunta da kowa ya sanya hannunsa a cikin lamarin ba.

 

3829689

 

 

 

 

captcha